1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta yi alƙawarin aiwatar da canje canje biyo bayan gagarumar zanga-zanga

August 7, 2011

Gwamnatin ƙasar ta Isra'ila ta ba da sanarwar gaggauta ɗaukar matakan canje canje don biyan buƙatar masu zanga-zangar.

Dubun dubatan 'yan Isra'ila ne suka shiga zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a birnin Tel AvivHoto: dapd

Bayan wata gagarumar zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Isra'ila, gwamnatin ƙasar ta ba da sanarwar ɗaukar matakan sauye sauye. A cikin jawabin da yayi ta rediyo, ministan kuɗi Juwal Steinitz ya ce za a gagauta aiwatar da matakan. Ya ce nan gaba kaɗan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai kafa wani kwamiti na musamman da ya ƙunshi ministocin da ƙwararrun masa, domin duba buƙatun masu zanga-zangar waɗanda suka fusata game da hauhawar kuɗin hayar gida, tsadar rayuwa, ilimi kiwon lafiya da kuma ƙaruwar bambamcin wadata tsakanin masu kuɗi da matalauta, inji wannan matar da ta shiga zanga-zangar.

"A yau mune lambawan na dake fuskantar makeken giɓi tsakanin mai kuɗi da talaka. Abin da muke gani a wannan yammacin da ma makonnin nan shi ne matsalar ta kai mana iya wuya."

Kimanin mutane dubu 350 ne suka shiga cikin zanga-zangar dake zama irin ta farko mafi girma a birninTel Aviv.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal