1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta yi barazanar sabunta hari kan Hezbollah

Abdul-raheem Hassan
November 3, 2025

Firaiminista Benjamin Netanyahu ya sha alwashin zafafa hare-hare kan kungiyar Hezbollah in gwamnatin Lebanon ba ta cika alkawarin kwace makaman kungiyar ba.

Israel Jerusalem 2025 | Benjamin Netanjahu bei Gedenkzeremonie für Gefallene des Eisenschwerter-Krieges
Firaiministan Isra'ila, Benjamin NetanyahuHoto: Alex Kolomoisky/REUTERS

Firaminista Benjamin Netanyahu, ya zargi kungiyar Hezbollah na kokarin sake jan damarar shirya makaman ta, kuma Israel za ta dauki matakin kare kanta bisa kaʼida idan hakan ta faru.

Ministan tsaron Isra'ila Katz a wata sanarwa da ya fitar ya ce "Hezbollah na wasa da wuta, kuma shugaban Lebanon yana jan kafa." Ya kara da cewa "Dole ne a aiwatar da kudurin gwamnatin Lebanon na kwance damarar kungiyar Hizbullah da kawar da ita daga kudancin kasar. Za a ci gaba da aiwatar da aikin da aka fara, kuma za a yi shi da karfin gaske. Ba za mu zuba ido mu bar wata barazana ga mazauna arewacin kasar ba."

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da kasashen biyu suka cimma a watan Nuwamban 2024, Isra'ila ta ci gaba da girka dakarunta a yankuna biyar a kudancin Lebanon kuma ta ci gaba da kai hare-hare akai-akai.

Yanzu haka, an tilasta wa dubban ‘yan Isra’ila da ke zaune kusa da kan iyakar arewacin kasar da Lebanon barin gidajensu na tsawon watanni bayan Hezbollah ta fara harba rokoki cikin Isra’ila bayan barkewar yakin Gaza a watan Oktoban 2023.

Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya ce Hezbollah na kokarin sake shirya kanta. "Muna sa ran gwamnatin Lebanon za ta cika alkawarin da ta dauka na kwance damarar Hezbollah, amma a fili yake cewa za mu yi amfani da 'yancinmu na kare kai bisa sharuddan tsagaita bude wuta," abin da Netanyahu ya fadawa majalisar ministocin kasarsa a taron mako-mako.

Luguden wuta tsakanin Isra'ila da Hezobollah na tsawon watanni biyu, kafin a amince da tsagaita bude wuta a bara. Kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, ta samu rauni sosai sakamakon yakin amma haryanzu tana da makamai da kudaden gudanarwa.

A watan Satumban 2024, Isra'ila ta kashe shugaban kungiyar Hassan Nasrallah, tare da wasu man'yan jagorori da dama. Tun bayan tsagaita bude wuta, Amurka ta kara matsa lamba kan mahukuntan Lebanon na su kwance damarar kungiyar, matakin da Hezbollah da kawayenta ke adawa da shi.

Gwamnatin Labanon ta tsara wani shiri na hana mallakar makamaiga wadan da ba sojojin gwamnati ba, kuma ta ce sojojin kasar sun fara aiwatar da shi tun daga kudancin kasar. Amma daga baya Shugaban kasar Joseph Aoun ya zargi Isra'ila da mayar da hannun agogo baya ta hanyar zafafa kai hare-hare, wanda na baya bayan nan ya kashe mutane hudu a gundumar Nabatiyeh, a cewar ma'aikatar lafiya ta Lebanon.