1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta yi ikirarin kashe Ali Larijani

March 17, 2026

Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta sanar da kashe wasu manyan jami'an gwamnatin Iran a wasu hare-hare ta sama da aka kai birnin Teheran cikin daren Litinin.

Shugaban majalisar tsaron Iran Ali Larijani
Shugaban majalisar tsaron Iran Ali LarijaniHoto: Courtney Bonneau/SIPA/picture alliance

Ministan tsaron Isra'ila Israel Katz, ya sanar a Talatar nan cewa an kashe Ali Larijani, daya daga cikin manyan shugabannin Iran, tare da Janar Gholamréza Soleimani, kwamandan rundunar Bassidj, bayan hare-haren da sojojin kasarsa suka kai a cikin daren jiya a birnin Teheran.

A cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa Katz ya bayyana cewa shugaban rundunar soji Isra'ila ya tabbatar masa da mutuwar Larijani, wanda shi ne sakataren Majalisar Tsaron Iran, da kuma Soleimani, shugaban rundunar Bassidj, wadda ake kallon ta a matsayin hukumar da ake amfani da ita don murkushe jama'a.

Tun bayan mutuwar Khamenei, Larijani ya kasance daya daga cikin manyan kusoshi a gwamnatin Iran, kuma ana daukar sa a matsayin wanda ke yanke manyan shawara tare da jagorantar hare-hare da ake kai wa Isra'ila da kasashen yankin Gulf.

Sai dai har kawo wannan lokaci hukumomin Iran ba su gaskata ko kuma musanta wannan labari ba, hasali ma an wallafa wata wasika daga shufukan Ali Larijani na X da kuma Instagram domin girmama sojojin Iran da suka mutu a yakin da kasar ke fafatawa da kawancen Amurka da Isra'ila.