Isra'ila ta yi ikirarin yin raga-raga da maboyar Khamenei
March 6, 2026
Sojojin Isra'ila sun ce a ranar Juma'a jiragen yaƙinsu sun tarwatsa maboyar karkashin kasa ta jagoran Addinin Iran Iran, marigayi Ayatollah Ali Khamenei.
Sojojin sun bayyana cewa wannan maboyar da ke ƙarƙashin ƙasa, wanda ke can ƙarƙashin harabar hedkwatar shugabancin gwamnatin Iran a tsakiyar Tehran, an tanade ta ne domin Khamenei ya riƙa amfani da ita a matsayin cibiyar ba da umarni ta gaggawa mai ciakakken tsaro.
Yaki tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila na kara kazancewa
Sun ƙara da cewa an kashe Khamenei kafin ya samu damar amfani da maboyar a yayin farmakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran.
Ko da yake sun kara da cewa duk da an kashe Khamenei amma maboyar ta ci gaba da kasancewa wurin da manyan jami’an gwamnatin Iran ke amfani da shi.
Iraki na iya fin kowace kasa gamuwa da matsaloli saboda yakin Iran
Sojojin Isra’ila sun ce kimanin jiragen yaƙi 50 ne suka kaddamar da hare-hare kan cibiyar wacce ke karkashin kasa a tsakiyar Tehran.