Isra'ila ta yi martani bayan wasu hare-hare daga Iran
March 20, 2026
Rundunar sojin Isra'ila ta ba da labarin ci gaba da kai hare-hare kan wasu muhimman kayayyakin more rayuwa a Tehran babbab birnin kasar Iran.
Hare-haren na zuwa ne yayin da da ‘yan kasar Iran ke shirin bikin Nowruz, wato sabuwar shekarar Farisa.
Da yammacin jiya Alhamis dai, Iran ta harba jerin makamai masu linzami zuwa Isra'ila, amma ba a samu rahoton asarar rayuka ba.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya shaida wa jaridar Times ta Isra‘ila cewa Iran ba ta da karfin kera makamai masu linzami ko tace sinadarin uranium bayan makonni uku na yaki.
A lokaci guda, kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait sun bayar da rahoton cewa an harbo makamai daga Iran da safiyar wannan Juma'a.
A wasu sassan yankin kuma, ma'aikatar tsaron Saudiyya ta ce ta dakile wani jirgin sama marar matuki a gabashin kasar, yayin da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta ce an kunna kararrawar gargadin hare-haren sama.