1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila da Hamas za su tattauna batun dakatar da yaki

Abdoulaye Mamane Amadou
July 4, 2024

Kasar Isra'ila ta amince da aika tawagar da za ta tattauna batun dakatar da yaki da kubutar da 'yan kasarta da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su a Gaza.

Hoto: Cohen-Magen/REUTERS

Isra'ila ta amince da aika tagawar sulhu da za ta tattauna batun sako 'yan kasarta da kungiyar Hamas ke ci gaba da garkuwa da su a yankin Gaza.

Karin bayani : Isra'ila ta tsagaita wuta na tsawon sa'o'i 11 a Gaza

Ofishin yada labarai na fadar firaministan kasar ya ce firaminista Benjamin Netanyahu, ya sanar da shugaban Amurka Joe Biden anniyarsa ta aike da tawagar ta musamman, da za ta duba batun sulhu da kungiyar Hamas da ma kubutar da Isra'ilawan da ke hannun Hamas, sai dai ofishin da ya fitar da sanarwar bai yi wani karin haske akai ba.

Ko da yake sanarwar ta kara da cewa firaministan ya bayyana cewa Isra'ila a shirye take ta kawo karshen yakin idan har ta kallama cimma daukacin manufofinta.

Karin bayani : Gangami adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu

Ko a wannan Laraba ma dai kungiyar Hamas mai iko da zirin Gaza, ta aike da wasu sharudanta ga masu shiga tsakani da ta gindaya wa Isra'ila kan batun tsagaita buda wuta a yakin da aka shafe watanni tara ana gwabzawa