1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a tsakiyar Beirut na Lebanon

Mouhamadou Awal Balarabe
October 11, 2024

Mutane 22 sun mutu yayin da 117 sun jikkata a luguden wuta da Isra'ila ta yi a babban birnin Lebanon, a cewar sabon rahoton ma'aikatar lafiya ta kasar. Sannan sojoji biyu na rundunar zaman lafiya ta MDD sun ji rauni.

Harbe-harben Isra'ila sun cimma gidajen fraren hula a Beirut na kasar Lebanon
Harbe-harben Isra'ila sun cimma gidajen fraren hula a Beirut na kasar LebanonHoto: Bilal Hussein/AP/picture alliance

 

Sojojin Isra'ila sun kai wasu munanan hare-hare guda biyu ta sama a yammacin Alhamis a tsakiyar birnin Beirut, baya ga harbe-harben da suka yi da suka jikkata mutane biyu a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD a  kasar Lebanon. Mutane 22 ne suka mutu yayin da 117 suka jikkata a wadannan hare-hare, a cewar wani sabon rahoton ma'aikatar lafiya ta Lebanon. Wannan dai shi ne karo na uku da rundunar sojin saman Isra'ila da ta fi mayar da hankali kan tungar 'yan Hezbollah, ke kai hare-hare kai tsaye a babban birnin Beirut tun bayan kaddamar da gagarumin farmakinta a Lebanon.

Karin bayani: Yara na kwana a kan titunan Beirut sakamakon rikici

Kasashen Turai da ke ba da gudummawar sojoji ga rundunar kiyaye zaman lafiya a Lebanon UNIFIL sun yi tir da harbe-harben Isra'ila, inda Italiya ta kira jakadan Isra'ila a Rome don nuna bacin ranta, yayin da shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel, wanda ya je kasar Laos don halartar taron shekara-shekara na ASEAN, ya yi Allah wadai da harbe-harben.

Karin bayani: 

Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga rundunar sojin Isra'ila kan hare-haren na ranar Alhamis. Amma kungiyar Hezbollah ta yi ikirarin lalata wani tankin yakin Isra'ila a Ras al-Naqoura kuma ta ce ta harba rokoki kan sojojin Isra'ilan da ke kan iyakar Lebanon da garin Maïs al-Jabal.