Isra'ila ta yi tayin hulda da Lebanon da SIriya
June 30, 2025
Kasar Isra'ila ta bayyana cewa tana shirye da kulla hulda ta diflomasiyya da kasashen Siriya da Lebanon da suka dade suna zaman doya da man ja, amma Isra'ila ta ce babu batun tattauna makoyar tudden Golan da ta kwace daga hannun Siriya.
Karin Bayani: Kasashen Isra'ila da Iran sun tsagaita wuta
Ministan harkokin wajen Isra'ila, Gideon Saar ya bayyana haka a wannan Litinin, sannan ya kara da cewa kaarsa tana da yakinin kan karya lagon kasar Iran lokacin fito na fito na tsawon kwanaki 12. Kuma lokacin ya yi da Isra'ila za ta kara kulla hulda ta diflomasiyya da kasashen yankin.
A shekara ta 2020 Isra'ila da kulla hulda da kasashe da dama na Laraba na Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain gami da Maroko da ke zama karo na farko, bayan wadda Isra'ila da kulla da Jodan a shekarar 1994, da kuma wanda aka fara yi da Masar a shekarar 1979.