1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kudus: Isra'ila ta yi wa Falasdinawa rusau

January 19, 2022

Irin wannan rusau din ne ya fara ruruta rikicin Isra'ila da Falasdinawa a watan Mayun shekarar da ta wuce. To amma hukumomin birnin Kudus sun ce sabon rusau din ba shi da alaka da abin da ya faru a 2021. 

Bulldozer in Jerusalem
Hoto: AP

'Yan sandan Isra'ila sun rusa wani fitaccen gidan Falasdinawa da ke a gabashin birnin Kudus. Rusau din da Isra'ilan ta aiwatar a wannan Laraba ya faru ne a unguwar da ake kira ''Sheikh Jarrah'', wace galibinta ta Falasdinawa ce. 


Hukumomi sun ce sun dauki matakin ne domin tun farko an gina gidan ba bisa ka'ida ba, kuma a yanzu gwamnati na son amfani da filin domin gina makaranta. A sakamakon hakan ma, 'yan sanda sun ce sun kama mutane 18 a lokacin da suka je rusa gidan.