1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila ta yi watsi da karar Afrika ta kudu

Abdullahi Tanko Bala
January 12, 2024

Israila ta yi watsi da zarge zargen da Afirka ta Kudu ta gabatar a kotun duniya da ke Hague na aikata kisan kare dangi a Gaza

Shari'a a kotun duniya da ke Hague
Hoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

Mai bai wa ma'aikatar harkokin wajen Israila shawara kan harkokin shari'a Tal Becker ya ce babu tushe a ikrarin Afirka ta Kudu kuma tuhumar tamkar cin fuska ne.

Ya shaidawa alkalai a kotun cewa Hamas ita ce ke da alhaki na halin kunci da mutanen da yaki ya ritsa da su a Gaza  suke ciki yana mai cewa Israila ta na yaki ne da Hamas amma ba da al'ummar Falasdinawa ba.

Ya kara da cewa Isra'ila ta yi amfani da 'yancinta ne na kare kanta bayan harin da Hamas tare da wasu Falasdinawa masu tsattsauran ra'ayi suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba inda suka hallaka mutane 1,200 da kuma yin garkuwa da wasu 'yan Israilar 250 wadanda rabin adadin har yanzu ba a sako su ba.

Karin Bayani: ICC ta ce toshe agajin Gaza laifin yaki ne

Wannan dai shi ne karon farko da aka gurfanar da Israila a gaban kotun duniya kan zargin kisan kare dangi

A rana farko ta sauraron shari'ar, Afirka ta kudu ta gabatar da bahasi inda ta nuna Israila ta kudiri aniyar aikata kisan kare dangi tare da bayar da misalai da hujjoji daga kalaman 'yan siyasar Israila.

Falasdinawa fiye da 23,000 sojojin Israila suka kashe a farmakin da suka kai Gaza yawancin su mata da kananan yara a cewar hukumar lafiya da ke karkashin ikon Hamas a Gaza.