1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Watsi da sauya dokar zama dan kasa

July 6, 2021

Majalisar dokokin Isra'ila ta yi fatali da dokar baiwa Palasdinawa masu auren yahudawa shedar zama dan kasa.

Symbolbild - Neuwahlen in Israel
Hoto: Getty Images/AFP/G. Tibbon

Majalisar dokokin Isra'ila a wannan Talatar ta kada kuri'ar kin amincewa da sauya dokar nan mai cike da sarkakkiya da ta hana bayar da shedar zama dan kasa ga Palasdinwan da ke yanki zirin Gaza masu auren Yahudawa ko kuma yan asalin kasar.

Batun hakan na zama wani tarnaki na farko da gwamnatin hada ka kalkashin jagorancin sabon firaministan kasar Naftali Bennett ta fara cin karo da shi. Majalisar ta Knesset ta gaza cimma wannan kudurin na sauya ayar dokar ta shekara ta 2003.

Dubun-dubatar iyallai ne dai wannan dokar ke yin mummunan tasiri a kansu shekara da shekaru.