Isra'ila: Za a rantsar da Netanyahu
December 29, 2022Talla
Bayan kwashe tsawon kimanin watanni biyu da gudanar da zaben majalisar dokokin isra'ila, a wannan Alhamis din ake sa ran rantsar da sabuwar gwamnatin Benjamin Netanyahu a birnin Kudus.
Ana dai ganin gwamnatin ta hadaka da za a rantsar, mai cike da 'yan siyasa masu tsattsaurar ra'ayi wanda ke tayar da hankulan jama'a. Sabuwar gwamnatin dai ta yi ikrararin cewa za ta kawo sauyin siyasa, sai dai kwararru na cewa sauyin zai iya haifar da soke shari'ar cin hanci da Netanyahu ke fuskanta.
Wannan dai shi ne karo na shida da Netanyahu zai kasance kan mulkin Isra'ila.