1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadada matsugunan Yahudawa

Yusuf Bala Nayaya
July 27, 2018

Wani matashi dai Bafalasdine ya tsallaka shinge inda afka yankin da Yahudawan suke zaune ya rika daba masu wuka, hakan ya sa Isra'ila daukar wannan mataki.

Symbolbild Israel Siedlungen im Westjordanland
Hoto: picture-alliance/newscom/D. Hill

Isra'ila ta bayyana aniya ta sake gina sabbin matsugunan Yahudawa daruruwa a yammacin kogin Jodan, matakin da ke zuwa bayan da wani Bafalasdine ya halaka Bayahude guda da raunata wasu uku. Ministan harkokin tsaron Isra'ila Avigdor Lieberman ya bayyana haka a wannan rana ta Juma'a.

"Amsa mafi kyau a yaki da ta'addanci shi ne fadada matsunan Yahudawa" bayanin kenan da Lieberman ya wallafa a shafinsa na Twitter. Ya ce za su gina gidaje 400 a yankin Adam  da ke a arewacin Birnin Kudus. Wani matashi dai Bafalasdine ya tsallaka shinge inda afka yankin da Yahudawan suke zaune ya rika daba masu wuka, lamarin da ya yi sanadin rai na guda daya sauran ukun kuwa suka sami raunika.