Isra'ila za ta jibge 'yan sanda a Al-Aqsa lokacin Ramadan
February 16, 2026
Rundunar 'yan sandan Isra'ila, ta sanar da shirinta na jibge jami'anta a harabar masallacin Al-Aqsa da kewaye, a lokacin azumin watan Ramadan da ke dab da kamawa, to sai dai hukumomin Falasdinu sun zargi Israilan da yunkurin shinge musulmi daga masallacin.
Bisa al'ada a duk lokaci irin wannan, dubban Falasdinawa ne ke ziyartar masallacin mai tsarki da ke birnin Kudus, domin yin ibada, wanda Isra'ila ta mamaye tun a shekarar 1967.
karin bayani - Isra'ila ta binne gawar karshe da aka dawar daga Gaza
Tuni dai jami'an tsaro suka fara daukar matakin takaita zirga-zirga a masallacin, bayan hana jami'ai 33 na gidauniyar Waqf ta kasar Jordan shiga, wadanda su ke aikin hidimtawa masallacin.
Inda aka dakatar da su daga aikin kafa rumfuna da wuraren duba marasa lafiya na wucingadi, kamar yadda suka saba gudanarwa.