Isra'ila za ta kare matsayarta a kotun duniya
May 17, 2024Afrika ta Kudu ta bukaci kotun duniya da ta gaggauta dakatar da Isra'ila daga farmakin da take kai wa fararen hula a Rafah, duk da a gefe guda Isra'ilan ta ce ta kaddamar da farmakin ne da zummar murkushe mayakan Hamas. Hukumomin Tel Aviv sun sha kare matsayarsu na yakin Gaza tare da watsi da zargin Afrika ta Kudu inda suka ce zargi ne mara tushe.
Karin bayani: Isra'ila: Kotun kasa da kasa za ta yanke hukunci
Duk da bukatar babbar kawar Isra'ilan wato Amurka na dakatar da kai hare-hare kan birnin Rafah saboda dalilai na jinkai da kuma dubban Falsdinawan da ke zaune a yankin, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kafe kan ci gaba da kai farmakin duk da hadarin da hakan ka iya jefa fararen hula.
Karin bayani: Israila ta yi watsi da zargin kisan kare dangi a Gaza
Hukumomin Pretoria sun gabatar da daftarin bukatu guda uku a gaban kotun na ICJ da suka hadar da bukatar gaggauta dakatar da Isra'ila daga kai hare-hare a Rafah da janyewar sojojin Isra'ilan daga yankin Gaza baki daya sai kuma bukatar shigar da kayan agajin jinkai a yankin.