Netanyahu zai mallaka wa Isra'ila yankin Palasdinu
September 1, 2019Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda ke zawarcin kuri'ar masu ra'ayin kishin kasa a zaben 'yan majalisar dokoki na ranar 17 ga wannan wata na Satumba a kasar ta Isra'ila, ya jaddada aniyarsa ta mallaka wa isra'ila garuruwan kama wuri zauna wadanda Yahudawa suka gina a matsugunnan Falasdinawa a yankin yammacin kogin Jodan da isra'ila ta mamaye.
Firaminista Netanyahu ya bayyana wannan aniya tasa ce a wani jawabi da ya gabatar a gaban jam'a a garin Elkana daya daga cikin garuruwan kama wuri zauna ta Yahudawa suka gina a yankin yamamcin kogin Jodan da Isra'ila ta mamaye.
Firaministan kasar ta Isra'ila dai na hankoran samun kuri'u ne daga kungiyoyin Yahudawa 'yan kishin kasa da sauran kananan jam'iyyu domin kayar da abokin hamayyarsa Benny Gantz a zaben na tafe. Yahudawa sama da dubu 600 ne ke rayuwa a yau a yankin yammacin kogin Jodan da kuma gabashin birnin Kudus da Isra'ilar ta mamaye.