1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ISRA'ILA ZA TA SAKO MORDECHAI VANUNU DAGA GIDAN YARI

YAHAYA AHMEDApril 20, 2004

Gobe ne za a sako Mordechai Vanunu daga gidan yari, bayan ya shafe shekaru 18 yana daure. Duk da sako shi da za a yi goben dai, gwamnatin Isra’ilan ta shimfida masa sharudda da dama, a cikinsu har da hana shi samun hulda da baki, da kauce wa duk wasu filayen jirgin sama da tashoshin jiragen ruwan kasar, da hana shi ficewa daga kasar da kuma zuwa ofisoshin jakadancin kasashen ketare a Isra’ilan. Bugu da kari kuma an hana shi yin amfani da tarhon salula da kuma yin amfani da shafin Internet wajen sadaswa.

Jami'an tsaron Isra'ila da dan sarka a gidan yari.
Jami'an tsaron Isra'ila da dan sarka a gidan yari.Hoto: AP

A cikin watan Oktoban 1986 ne jaridar nan "Sunday Times" ta kasar Birtaniya, ta buga wani rahoto wanda ke ba da bayanai dalla dalla kan cibiyar makamashin nukiliyan Isra’ila, da kuma irin makaman kare dangin da ta ke mallaka. Tushen wannan rahoton dai shi ne Mordechai Vanunu, wanda a lokacin yake da shekaru 31 da haihuwa. Vanunun dai ya yi aiki har tsawon shekaru 9, a cibiyar makamashin nukiliyan Isra’ilan da ke garin Dimona. Yoel Cohen, wani masanin fannin harkokin siyasa, wanda kuma ya rubuta littafi kan wannan batun na Vanunu, ya bayyana cewa:-

"A lokacin da Vanunun ke aikin dare a cibiyar, ya kuma yi karatun Falsafa a jami’ar Ben Gurion. Yayin wannan karatun ne ya fahimci cewa, akwai sabani tsakanin ra’ayin da yake bi da kuma aikinsa na wannan lokacin – wato shi mai fafutukar neman zaman lafiya, ga shi kuma yana aiki a kafar sarrafa makaman kare dangi."

Kafin hakan ma, Vanunu ya shiga cikin zanga-zangar da wasu `yan Isra’ilan suka yi, ta nuna adawa ga afka wa Lebanon da yaki da dakarun Isra’ila suka yi a shekarar 1982. Tun daga wannan lokacin ne ya dinga daukan hotunan cibiyar, a ko yaushe ya tafi aiki. Kamar dai yadda Cohen ya bayyanar:-

"Ya dau hotunan sirri 57, na na’urorin sarrafa makamai na cibiyar. Amma a lokacin, wato 1985, bai san abin da zai yi da su ba tukuna. A cikin watan Ifirilun 1986 ne, aka yi mummunan hadarin nukiliyan nan na Tschernobyl a kasar Tarayyar Soviyet. To daga nan ne fa, ya ga cewa, ya kamata ya bankada wannan sirrin, don ya sanad da duniya cewa ga abin da Isra’ilan ma ke boye da shi".

A cikin 1985 din ne dai aka sallami Vanunun daga aiki a wannan cibiyar. Daga bisani ne kuma ya yi kaura zuwa Austreliya, inda ya sake addini, ya zamo kirista na darikar Anglikan. Limamin wannan darikar dai na cikin masu bin ra’ayin nuna adawa ga makaman nukiliya. Hakan kuwa ya gamsad da Vanunun sosai. Ta kan wani dan jarida ne kuma ya sami hulda da jaridar Sunday Times ta Birtaniya. Vanunun da kansa, ya bayyana cewa:-

"Na dai ci gaba da bin ra’ayina, tare da yin imanin cewa, ko me mutum ya ga yana da amfani ga halin rayuwar dan Adam, to kamata ya yi ya ba da tasa gudummuwa wajen cim ma wannan gurin, ko da ma a wasu lokutan, zai sadaukad da ransa ne wajen yin hakan."

Kwanaki kadan bayan bankada wannan sirrin da jaridar "Sunday Times" ta yi ne, wata jami’ar kungiyar leken asirin nan Mossad ta Isra’ilan ta shawo kan Vanunun har suka tashi daga London zuwa birnin Rum, inda daga a nan aka sace shi zuwa Isra’ila. Daga bisani ne kuma kotun Isra’ilan ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru 18 a gidan yari, saboda zargin da ake yi masa na leken asiri da cin amanar kasa. A lokacin da yake daure dai, an nuna masa cin mutunci iri-iri. Shi ne dai, wanda aka taba tsarewa a dakin sarka shi kadai har tsawon shekaru 12, a tarihin `yan sarka na kasashen Yamma. Sabili da hakan ne ma kungiyar fafutukar kare hakkin dan Adam nan Amnesty International, ta zargi gwamnatin Isra’ilan da zalunci da kuma cin zarafin Vanunun.

A halin yanzu dai, Vanunu ya zamo jarumi saboda bayyana wa duniya a karo na farko, sirrin makaman nukiliyan da Isra’ila ta mallaka.

Marubuci Cohen, ya bayyana cewa, a nasa ganin dai:-

"Rufa-rufa da ake yi kan makaman nukiliya, ba za ta taba samun jituwa da ra’ayin jama’a a kasar da ake tafiyad da mulkin dimukradiyya ba."