1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila za ta shiga sabon babi na yaki a Zirin Gaza

October 15, 2023

Isra'ila na shirin fara kaddamar da munanan hare-hare a zirin Gaza daidai lokacin falasdinawa ke tsere wa yankunansu saboda farmakin da Isra'ilar ke kai musu.

Hoto: Ariel Schalit/AP/picture alliance

Rundunar sojan Isra'ila, ta bayyana shirinta na kaddamar da hare-hare ta sama da kasa da ma ta ruwa a yankin zirin Gaza.

Da yammacin jiya Asabar ne rundunar dakarun na Isra'ila ta sanar da cewa tana kan jibge mayakanta domin shiga wani babi na yaki da ke faruwa tsakanin kasarta da mayakan kungiyar Hamas. Mayakan na Isra'ila dai na nuna cewa za su bayar da karfi ne a hare-hare ta kasa.

Dubban mazauna yankin Falasdinu ne dai suka kaura daga yankin arewaci zuwa kudanci, bayan umurnin da Isra'ila ta bayar na cewar fararen hula su yi hakan. Sai dai kuma kasashen duniya sun yi tir da umurnin na Isra'ila.

Sama da mutum 1,300 ne suka mutu a Isra'ila a harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar Asabar ta makon jiya abin da ya haddasa yakin da ake ciki.

Ma'aikatar lafiya a yankin falasdinu kuwa, ta ce sama da mutane 2,200 hare-haren Isra'ila suka kashe a zirin Gaza kawo i yanzu.

Ita kuwa Saudiyya ta dakatar da duk wata tattaunawar dawowa da huldar diflomasiyya a tsakaninta da Isra'ila, daidai lokacin da tashin hankali ke kara kazanta a zirin Gaza.

Da ma dai a 'yan watannin nan ne kasashen biyu sun tasamma kafa tarihin dawo da alaka a tsakaninsu, kafin kuma tashin tashin tashinar da ake ciki a tsakanin Isra'ila da Gaza da ta kunno a ranar Asabar ta makon jiya.