Isra'ila za ta shiga sulhun Masar bayan kashe jami'an jinkai
April 6, 2024Jaridar Masar ta Al-Qahera ta ce shugaban hukumar CIA na Amurka Bill Burns da Firaiministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani za su kasance a wajen zaman sulhun domin kawo karshen yakin na Gaza.
Karin bayani: Isra'ila ta kori sojojinta 2 da ladaftar da wasu 3 da suka hallaka jami'an agaji 7 a Gaza
Tattaunawar sulhun na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta amsa laifinta tare da daukar mataki na sallamar sojojinta biyu daga bakin aiki, bayan kashe jami'an agajin jinkan nan bakwai na 'World Central Kitchen', a daidai lokacin da suke tsaka da gudanar da aikin jinkai a Gaza.
Karin bayani: Isra'ila ta ce bisa kuskure ta kashe jami'an agaji a Gaza:
Mayakan na Hamas tun bayan kaddamar da harin 7 ga watan Oktobar bara, sun yi garkuwa da 'yan Isra'ila kimanin 250 da har yanzu 130 na hannunsu, yayinda mutane 1,170 suka mutu. Kazalika Ma'aikatar lafiyar Falasdinu ta ce Isra'ila ta hallaka kimanin mutane 33,137 a Gaza da galibinsu mata da kananan yara.