SiyasaGabas ta Tsakiya
Daftarin tsaron Zirin Gaza
February 23, 2024Talla
Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya gabatar da taswirar farko a hukumance bisa tsarin yankin Zirin Gaza na Falasdinu bayan yakin da ke faruwa, inda gwamnatin Isra'ila za ta ci gaba da kula da harkokin tsaron duk yankunan Falasdinawa na yankin tare da sake gina Gaza da kawar da harkokin makamai a yankin baki daya.
Tsarin ya kuma kunshi cewa Isra'ila za ta ci gaba da tafiyar da tsaron yankin gabar yamma da kogin Jodan.
Tun ranar Talata da ta gabata Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya gabatar da daftarin ga majalisar tsaron kasa, wadda za ta iya kawo sauye-sauye ga matakan kuma a wannan Jumma'a kamfanin dillancin labaran Reuters ya ga kunshin daftarin na matakan da Isra'ila za ta dauka kan tsaron bayan yaki.