Isra'ira ta yi fatali da kashedin Majalisar Dinkin Duniya
December 28, 2016Talla
Zaman taron zai yi nazarin bayar da takardun izinin gine-ginen daruruwan gidaje a unguwanni uku na gabashin Birnin Kudus a yankin Falasdinawa da Isra'ilar ta karbe ta kuma gama da nata a cewar wata kungiya mai zaman kanta ta kasar ta Isra'ila da ke yaki da mamayar da kasarsu ke yi wa Falasdinawa.
Mataimakin magajin garin Birnin Kudus Meïr Turgeman, ya ce kuri'ar da aka kada a ranar Juma'a a Majalisar Dinkin Duniya da ta haramta manufar gina matsugunan Yahudawa a yankunan Falasdinwa, ba za ta hana wannan taro nasu da suka dade da tsarawa ba. Membobi 14 daga cikin 15 na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ne dai suka kada kuri'ar nuna adawarsu tare da neman Isra'ila ta dakatar kai tsaye da mamayar da take yi wa Falasdinawa.