Nijar: Zargin Issoufou da cin-hanci
May 9, 2023A cikin wata wasika da kungiyar ta M62 ta rubuta ta kuma shigar a gaban hukumar ta HALCIA a ranar takwas ga wannan wata na Mayu, ta bukaci a gudanar da bincike kan tsohon shugaban kasar jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou wanda rahoton wata jaridar kasa da kasa ta "Africa Intelligence" da ke da cibiya a birnin Paris na Faransa, ta zarga da karbar wani haramtaccen kamasho na kudi miliyan dubu biyu da 600 na dalar Amurka da kamfanin Energy Standard Trading FZE ya zuba masa a wani asusun banki na kamfanin Standard Chartered na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan lamarin ya wakana ne a wani cinikin bayan fage na ton 2,500 na ma'adinin uranium mai cike da sarkakiya da kamafinin SOPAMINE ya yi a shekara ta 2011 zuwa 2012 da kamfanin Areva na Faransa dakuma kasar Amurka, cinikin da daga karshe Amurka da kamfanin na Areva na Faransa suka tafka munmunar asara a cikinsa.
#b#Malam Sanoussi Mahaman jagoran rikon kwarya na kungiyar ta M62 ne, ya shigar da wannan kara a gaban HALCIA. To sai dai da yake mayar da martini, Malam Assoumana Mahamadou kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki kana daya daga cikin na kusa da tsohon shugaban kasar, ya ce zargin da kungiyar ta M62 ta yi bas hi da tushe kuma ta yi shi ne da nufin bata masa suna kawai. Hukumar ta HALCIA dai ta tabbatar da karbar wannan kara, sai dai wasu masana dokoki na ganin da wuya karar ta yi tasiri ganin cewa dama kungiyoyin farar hula na Nijar sun shigar da kara kan wannan badakala ta cinikin uranium a gaban kotu kuma a bisa dokokin HALCIA ba ta da izinin karbar kara matsawar batun na a gaban kuliya. Haka kuma tsohon shugaban kasar na da rigar kariya wacce kotun koli kadai ce ke iya fidda mass ita idan ta same shi da laifin cin amanar kasa, kuma kafin kotun ta dauki wannan mataki sai da amincewar kaso biyu cikin uku na 'yan majalisar dokokin kasar ta Nijar.