ISWAP ta dauki alhakin halaka kiristoci a Arewacin Najeriya
April 22, 2025
Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta yi ikirarin daukar alhakin munanan hare-haren da aka kai kan sansanonin jami'an tsaro, da kuma fararen hula kiristoci a yankin Arewacin Najeriya, a farkon watan Afirilun 2025.
Wannan na cikin sakonni bakwai da kungiyar ta wallafa a kafar yada labaranta ta Amaq, ciki har da fayafayan bidiyo biyu da kundin hotunan da ke zayyana yadda suka kitsa hare-haren ta'addancin.
Karin bayani:ISWAP ta kashe jami'an tsaron Najeriya
Daga cikin hare-haren har da wanda suka kai kan barikin sojoji na garin Yamtage da suka kona a jihar Borno, bayan halaka sojoji uku, sannan suka kama jami'an sa-kai hudu da ke aiki da sojojin suka kashe a jihar.
Karin bayani:Nakiya ta hallaka mutum 10 a Najeriya
Haka zalika a jihar Adamawa sun kai hare-hare biyu a kauyukan Lareh da Banga, da mafi akasarin al'ummarsu kirsitoci ne, suka kashe mutane biyu suka kona gidaje 30 da kuma majami'a daya, kamar yadda suka wallafa hotunan a jaridarsu, har ma da lalata motar 'yan sanda bayan jikkata su.