SiyasaAfirka
ISWAP ta kashe jami'an tsaron Najeriya
November 30, 2023![Motar mayakan kungiyar Boko Haram](https://static.dw.com/image/55769335_800.webp)
Talla
Wani harin kwanton bauna da ake zargin na mayaka masu ikirarin jihadi ne, ya yi sanadin salwantar jami'an tsaron Najeriya akalla hudu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Mayakan na tarzoma da ke da alaka da kungiyar IS, sun bude wuta ne a kan ayarin sojoji hadi da wasu 'yan sa-kai da ke kan hanyarsu ta komawa garin Mongono, mai tazarar mil 87 da Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.
Hare-hare na mayakan da ke ikirarin jihadin dai sun kashe dubban mutane yayin da wasu miliyoyi suka rasa sukuni tun bayan bullar matsalar a shekara ta 2009.
Matsalar tsaro dai gagarumar matsala ce daga cikin kalubalan da gwamnatin Bola Tinubu da ta kama aiki cikin watan Mayun bana ke fuskanta a Najeriyar.