ISWAP tayi garkuwa da ma'aikatan gwamnatin Borno
December 2, 2021Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Najeriya suka ce sun hallaka wasu mayakan ISWAP da Boko Haram da dama a jihohin Borno da Yobe. Harin na ranar Larabar da ta gabata, ta rutsa da ma’aikatan guda shida ne a kan hanyar da ake yi a tsakanin garuruwan Damboa da Chibok da ke fama da matsalolin tsaro.
Ya zuwa yanzu babu labarin inda aka kai wadannan ma’aikata ko kuma halin da suke ciki inda iyalai da ‘yan uwa da abokan arziki suka fada cikin tashin hankali. Gwamnatin jahar Borno ta bakin kwamishinan aiyuka na jahar Yerima Saleh ta tabbatar da labarin kame jami’an guda shida da wasu motoci mallakar gwamnatin guda biyar da suka sace.
Karin Bayani: ISWAP ta sako ma'aikatan agaji da ta kama
Kokarin ji daga bakin iyalan wadannan ma’aikata wanda yanzu ke cikin tsananin tashin hankali ya ci tura. Wani abu da kame ma’aikatan ya fito da shi, shi ne karuwar tabarbarewar tsaro musamman a yankuna kudancin jahar Borno inda kusan a kullum sai an samu rahoton kai hari ko dai kan jami’an tsaro ko kuma fararen hula matafiya.
A bangaren daya kuma sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram da ISWAP da dama bayan wasu jerin hare-hare da suka kai a Gajiram a jahar Borno da kuma Buni Yadi a jihar Yobe. Baya ga Sojojin da suka aiyana nasarar hakan al’ummar da ke yankuna ma sun tabbatar da samun wannan nasarar.
Karin Bayani: Najeriya ta tabbatar da kisan al-Barnawi
Yayin da ake fuskantar karuwar tafiye-tafiye a wannan watan na Disamba a saboda bukukuwan da aka sa a gaba, mutane na baiyana damuwa saboda yadda hanyoyi a jahohin Arewa maso Gabashin Najeriya suka zama tarkon na mayakan Boko Haram da ISWAP da ke fitowa suna kame mutane don yin garkuwa da su.