1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Giorgia Meloni ta sha rantsuwar kama aiki

Binta Aliyu Zurmi
October 22, 2022

Giorgia Meloni ta jam'iyyar Brothers of Italy ta sha rantsuwar kama aiki a matsayin firaministar kasar wadda hakan ya sanya ta kasancewa mace ta farko da ta dare kan wannan kujera.

Regierungsbildung in Italien - Giorgia Meloni
Hoto: Gregorio Borgia/AP/dpa/picture alliance

Firaminista Meloni ta sha rantsuwar kama aiki ne a gaban shugaban kasar Sergio Mattarella a fadar Quirinal da ke da matukar tarihi a kasar.

Jam'iyyar Brothers of Italy da ke da nasaba da masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa a Italiya, sun samu nasarar kafa gwamnati a karon farko tun bayan yakin duniya na biyu.

Tuni sabuwar firaministar ta fitar da sunayen majalisar ministocinta da suka hada da mata 6, yayin da kasashen duniya tuni suka fara aike wa da sakon tayata murna.