1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya na fargabar sake bullar corona

Binta Aliyu Zurmi
July 3, 2020

Mahukunta a yankin Veneto da ke arewa maso gabashin Italiya sun bayana shirinsu na daukar tsauraran matakai dangane da annobar COVID-19 da yanzu haka ake fargabar sake bullar ta a karo na biyu.

Italien Brescia | Coronavirus: Drive-Through Corona-Test
Hoto: picture-alliance/Photoshot/M. Biatta

A makon gobe ne dai hukumomin suka ce za su fidda sabbin dokoki a yankin wanda ya hada da Venice, kuma sun ce za su yi hakan ne da nufin dakile bazuwar cutar.

Wannan matakin da ake shirin dauka dai na zuwa ne bayan da aka sami wani mutum dauke da cutar da  ya kuma ki ya kebe kansa, har ma ya kai ga yin mu'amala da muatnen da yawansu ya kai 89, 

kuma tuni aka tabbatar da cewa hudu daga cikinsu sun kamu da cutar yayin da shi kansa yanzu haka yake kwance cikin mawuyacin hali.