Daruruwan 'Yan gudun hijirar sun sami mafaka a Italiya
July 16, 2018Talla
Lamarin ya kawo karshen halin wahalar da daruruwan 'yan gudun hijirar suka tsinci kansu a kwanakin da suka kwashe suna zaune cikin kwalekwale a gabar ruwan kasar bayan da suka baro kasashensu na asali.
Kasashen mambobi a kungiyar EU sun amince da su karbi fiye da rabin 'yan gudun hijirar, a yunkurin dinke barakar da aka samu a tsakanin kasashen na mayar da wadannan mutanen Afirka. Dokar kasa da kasa, ta haramta mayar da 'yan gudun hijirar da suka tsere daga rigingimu masu hadari ga rayuwarsu kasashensu na asali.