1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Italiya ta bijire tayin Amurka na maye Iran a kofin duniya

April 23, 2026

Ministan wasanni na Italiya ya ce wannan sam ba shawara ce da ta dace ba, yayin da ministan kudi ya ce abin kunya ne ma

Shugaban Amurka Donald Trump tare da shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino a birnin Washington.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino a birnin Washington.Hoto: Andrew Harnik/Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya ta yi watsi da tayi da shugaban Amurka Donald Trump ya yi mata, na ganin ta maye gurbin Iran a gasar cin kofin duniya ta 2026, da za a gudanar a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Ministan harkokin wasanni na Italiya Andrea Abodi, ya ce wannan sam ba shawara ce da ta dace ba, yayin da shi ma ministan kudi na Italiya Giancarlo Giorgetti ya bayyana shawarar a matsayin abin kunya.

Karin bayani:FIFA ta ce Iran za ta je gasar cin kofin duniya ta Amurka 

Shi ko shugaban kwamitin Olympic na kasar, wanda ke da alhakin kula dukkan harkokin wasannin kasar Luciano Buonfiglio, cewa ya yi aikata hakan na zama wani babban laifi, domin cancanta ake bi sannan a samu damar zuwa gasar.

Jaridar The Financial Times ta rawaito cewa wani kusa a gwamnatin Amurka mai suna Paolo Zampolli, shi ne ya mika shawarar wannan zabi ga shugaba Trump da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino.

Karin bayani:Tasirin yakin Amurka a Iran akan wasanni 

Za a fara gasar a ranar 11 ga watan Yunin 2026, sannan a karkare a ranar 19 ga Yuli, to sai dai har yanzu Iran ba ta ce komai ba, game da shirin halartar gasar ko akasin haka, inda aka tsara buga wasanninta uku na rukuni a Amurka.