1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Taron Italiya da EU da kasashen Afrika

January 29, 2024

Kasar Italiya na karbar bakuncin wani taron koli da shugabanni kasashen Afrika a domin gabatar da sabin yarjejiyoyi a game da makamashi da kuma hadin gwiwa don shayo kan kwararar bakin haure i zuwa Turai.

Italiya ta shirya taron koli da shugabannin kasashen Afrika
Italiya ta shirya taron koli da shugabannin kasashen AfrikaHoto: Marta Clinco

Taron na wuni guda da za a gudanar a birnin Roma a karkashin firaministar Italiya Giorgia Meloni da shugabannin hukumomin Tarayyar Turai, zai bayyana wani tsari da ake yi wa lakabi da ''Tsarin Mattei'' wanda kamfanin samar da makamashi na Italiya ENI ya samar tun a shekarar 1950 wanda ya bayar da shawarar taimakawa kasashen Afrika a fannin bunkasa albarkatun da Allah ya huwace musu. A gefe guda kuma akwai yiwuwar taron ya tabo batun kasashen yankin Sahel guda uku da suka hadar da Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar dukanninsu da ke karkashin mulkin sojoji bayan da suka sanar da aniyarsu ta ficewa daga kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika ECOWASa ranar 28.01.2024.

Karin bayani: Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun yi bankwana da ECOWAS

Ana sa ran shugabanni kasashen Afrika akalla 25 da har yanzu ba a fitar da jerin sunayensu ba a hukumance za su halarci taron tare da wakilan hukumomin Malajisar Dinkin Duniya da na Tarayyar Afrika da kuma cibiyoyin raya tattalin arziki irin su Asusun ba da lamuni na duniya IMF.

A cewar jaridar Corriere della Sera, Italiya na iya ware wa wannan shirin zunzurutun kudi da ya kai miliyan hudu na Yuro domin bunkasa fannonin noma da sufuri da ababen more rayuwa da kuma uwa uba makamashi a cikin shekaru bakwai masu zuwa, abin da zai kara taimakawa wajen rage dogaro da Rasha a fannin Iskar Gas.