1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Italiya ta tsananta tsaro bayan harin Rasha

March 26, 2024

Italiya ta bi sahun Faransa wajen karafafa matakan ankararwa ta fuskar tsaro bayan harin ta'adda da aka kai gidan rawa a birnin Mosko na kasar Rasha a karshen makon jiya.

Dan sandan Italiya
Jami'an 'yan sanda na kasar ItaliyaHoto: Alberto Pizzoli/AFP/Getty Images

An cimma matakin ne bayan taron majalisar manyan masu hannu cikin al'amuran tsaron kasar da aka yi a birnin Rome.

Tuni ma aka tsara manyan matakan tsaro a wannan mako da ake gab da fara hidindimun Easter da mabiya addinin Kirista ke girmamawa.

A irin wadannan lokutan, Paparoma Francis kan kasance da ayyuka masu yawan gaske masu nasaba da lokacin na Easter a Rome da kuma fadar Vatikan.

Kungiyar ta'adda a duniya IS ta ce ita ta kai harin harin.

Ita ma Jamus ta bakin ministan harkokin cikin gidanta, ta nuna cewa barazana daga kungiyoyi na ta'adda matsala ce gagaruma.

A karon farko dai Shugaba Putin na Rasha ya amince cewa harin na da alaka da 'yan ta'adda, ammam kuma ya danganta su da kasar Ukraine.