Italiya za ta sayo iskar gas daga Afirka
April 20, 2022Talla
Ministocin kasar Italiya, za su kai ziyara kasashen tsakiyar Afirka a wannan Laraba, domin kulla yarjejeniyar cinikin iskar gas yayin da kasar ke kokarin dakatar da sayo makamashin daga Rasha.
Firaministan Italiya, Mario Draghi, na neman sanya kasar Angola da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango cikin jerin kasashen da za su cike gurbin Rasha.
Kasar na sa ran samun iskar ta gas da za ta kai akalla 45 cikin dari.
Ministocin na Italiya za su shiga kasashen na tsakiyar Afirka ne tare da rakiyar shugaban kamfanin hakar mai na kasar, wato ENI, Mr. Claudio Descalzi.
Haka ma akwai aniyar wata ziyarar daga Italiya zuwa kasar Mozambik cikin watan gobe na Mayu a game da wannan batu na makamashi.