Sudan: Zaman lafiya a birnin Khartoum duk da fada
February 13, 2026
Gwamnatin sojoji ta Sudan da kasashen duniya suka amince da ita, wadda Janar Abdel Fattah Burhan ke jagoranta, na kokarin nuna cewa al'amura sun fara komawa yadda suke a babban birnin kasar, Khartoum, bayan da aka kwashe cikin rikicin da ya nemi dai-dai-ta birnin.
A ranar Lahadi ne filin jirgin saman kasa da kasa na Khartoum ya karbi jirgin fasinja na farko da ya sauka a cikinsa a fiye da shekaru biyu. Jirgin ya taso ne daga Port Sudan da ke gabashin kasar a gabar tekun Bahar Maliya dauke da fasinjoji 160 ciki har da firaministan rikon kwarya na kasar, Kamil Idris. Mahukunta sun bayyana hakan a matsayin alamardai-daituwar al‘amura.
Iya sake gina Sudan
Tun a watan Afrilun 2023 ne rikicin neman iko tsakanin rundunar sojin Sudan wato SAF da kuma dakarun sa kai na Rapid Support Forces, RSF, ya rikide zuwa yaki. Rikicin ya samo asali ne daga sabani kan yadda za a hade RSF cikin rundunar sojin kasa. RSF ta samu iko da Khartoum, lamarin da ya tilasta wa gwamnati komawa Port Sudan mai nisan kusan kilomita 700 daga babban birnin.
Sai dai a watan Maris din 2025, rundunar sojin Sudan ta sake kwato galibin birnin Khartoum. Hukumar kula da hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, IOM, ta ce kimanin mutane miliyan 1 da dubu 300 daga cikin miliyan 3 da suka tsere daga Khartoum a 2023 sun koma birnin tun bayan sake kwato shi.
Gargadin Majalisar Dinkin Duniya
Mummunan artabun da aka gwabza daga Afrilu 2023 zuwa Maris 2025 ya lalata muhimman ayyuka kamar samar da ruwan sha da wutar lantarki. Har ila yau, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa har yanzu ba a kawar da nakiyoyi a wasu yankuna ba.
Duk da komawar gwamnati Khartoum, yaki na ci gaba a wasu jihohi ba tare da wata yarjejeniyar tsagaita wuta ba. Rikicin ya haddasa babbar matsalar gudun hijira a duniya, inda mutane kimanin miliyan 14 suka rasa matsugunansu.
A halin yanzu, yankin Kordofan ya zama cibiyar sabon rikicin. Sojojin Sudan sun ce sun sake kwato wasu garuruwa a Kordofan.
Abin da masana suke gani
Masana sun dade suna gargadin cewa Sudan na iya darewa zuwa kasashe biyu masu gwamnatoci masu adawa da juna, tare da samun goyon bayan kasashen waje daban-daban.
A bangaren jin kai kuwa, halin da ake ciki na kara tabarbarewa. Bob Kitchen, daraktan shirye-shiryen gaggawa na kungiyar International Rescue Committee, ya ce samun agaji ga mabukata na kara zama kalubale.
Duk da musanta zarge-zarge akai-akai, ana kallon Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin babbar mai goyon bayan dakarun RSF da jagoranta Janar Mohammed Hamdan Dagalo. A daya bangaren kuma, Masar da Turkiyya na mara wa gwamnatin Janar Abdel Fattah Burhan baya. Tuni kungiyar Taryyar Turai da Amurka suka lafta wa bangaorin da ke yaki da juna takunkumi, sai dai babu tabbas ko hakan zai kara hanzarta kawo karshen rikicin da ya lalata zaman lafiyar Sudan.