1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iyaye a Isra'ila sun nemi tsagaita wuta a Gaza

Abdullahi Tanko Bala
August 23, 2025

Yayin da sojojin Isra'ila ke shirin aiwatar da gagarumin farmakin karbe iko da zirin Gaza, iyaye da dangin 'yan Isra'ilar da Hamas ke tsare da su a Gaza sun nemi a tsagaita wuta don ceto rayuwar 'ya'yansu

Zanga zangar Tel Aviv na iyayen da ake tsare da 'ya'yansu a Gaza
Zanga zangar Tel Aviv na iyayen da ake tsare da 'ya'yansu a GazaHoto: Shir Torem/REUTERS

Dangi da iyalan 'yan Isra'ila da Hamas ke tsare da su a Gaza kusan shekaru biyu a yanzu sun bukaci gaggauta tsagaita wuta inda suka ce farmakin da sojojin Israila shirin afkawa a Gaza na iya janyo hasarar rayukan yayan nasu.

Suka ce tsawon kwanaki 687 'ya'yansu na tsare a Gaza.

Idan Netanyahu ya amince da wannan bukata zai fara tattaunawa don samun mafita.

A ranar Litinin da ta gabata Hamas ta sanar da cewa ta bai wa masu shiga tsakani a tattaunawar da ake yi martaninta na tsagaita wuta.