1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ja-in-ja kan tsarin jami'o'in gwamnati a Nijar

Gazali Abdou Tasawa MAB
September 15, 2022

Sabon takun saka ya kunno kai tsakanin gwamnatin Nijar da kungiyar malaman jami’o’i da ma ta dalibai kan garambawul da aka yi wa tsarin aikin jami’o’in kasar, lamarin da suka ce zai haifar da komabaya ga harkar ilimi.

Niger Niamey Studentenproteste
Bau darasi a jami'ar Niamey a lokacin zanga-zangar dalibaiHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Garambawul da gwamnatin Nijar ta yi ya tanadi tilasta wa jami'o'i da aka kafa a shekara ta 2014 a jihohin Dosso da Tillabery  da Agadez da Diffa komawa aiki inda kowacensu aka dora ta kan wani fannin ilimin da ya kamata ta mayar da hankali kansa, kamar bincike kan muhalli ko samar da tsaftatacce makamashi ko harkokin noma da kiwo. 

Sai dai gwamnatin ta ce jami'o'in sun bude fannonin koyar da wasu ilmomin na daban a cikinsu. Lamarin da ya haifar da cunkoso da sauran matsaloli na tafiyar da karatu a cikinsu. A kan haka ne gwamnatin ta Nijar ta yi wannan garambawul da nufin ganin kowace jami'ar ta koma aikinta na ainahi. Kana ta dauki matakin dauke wasu fannonin ilimi zuwa wasu manyan jami'o'in na Yamai, Tahoua, Maradi da Damagaram. Amma Dr Sahabi Bkasso, babban magatakardar kungiyar malaman jami'ar ta SNECS ya ce kungiyarsu ta yi fatali da matakin.

Daliban jami'ar Niamey na zanga-zanga a game da garambawul ga tsarin karatuHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Kungiyar Malaman jami'o'in kasar ta Nijar ta ce matakin zai sanya malaman jami‘ar da dama rasa aikinsu. Ita ma a nata bangare hadaddiyar kungiyar daliban kasar Nijar wato UNS tu nuna rashin amincewarta da mataki wanda ta bayyana a matsayin komabaya, a cewar Ibrahim Abdoulahi, sakataren kula da harkokin ilimi a kungiyar daliban kasar ta Nijar.

 

Kokarin da DW ta yi na jin ta bakin ministan ilimi mai zurfi na Jamhuriyar Nijar ya ci tura. Sai dai a wata hira da da shi kan wannan batu a makon da ya gabata, ya bayyana cewa matakin gwamnatin bai saba wa kowace ka'ida ba.

A shekara ta 2017 ma daliba sun yi zanga-zanga don neman hakkokinsuHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

" Gwamnati ita ce ke da hurumin yin duk wani tsari na tafiyar da jami'o'in kasa a yadda ta ga ya dace. Sannan wannan garambawul da muka yi, an tsara shi ne tare da shugabannin jami'o'in kasar a loakci wani zama na musamman a wannan ofishi nawa. Kuma ni ina ganin babu wani wanda zai ce ya fi wadannan mutane dacewa yin magana da sunan wadannan jami''oI na gwamnati."

Yanzu dai an shiga wani hali na mai abu ya rantse, maras abu ya rantse, a daidai lokacin da a makwabciyar kasa Najeriya ma karatu a jami'o'i yake tangadi a sakamakon yajin aikin takwarorinsu kungiyar ta SNECS A Najeriya wato ASUU.