Jack ma ya baiwa Najeriya kayan yaki da corona
March 25, 2020Talla
Jiirgi ya sauka dauke da kayayaki da suka hada da akwatunan gwajin cutar guda dubu ashirin da takunkumi guda dubu dari da rigunan rigakafi guda dubu a cewar Abdulaziz Abdullahi baban jami'i a hukumar lafiya ta kasar. Ya kara da cewar wannan gudumawa da suka karba za su rabawa ma'aikatan asibitoci da ma dakunan gwajegwaje.
Masana a fanin lafiya tuni sukai ta nuna damuwar su a kan Najeriya kasancewar kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka da kuma fanin lafiyar ke cikin mahuyacin halin.
Jack Ma ya taimakawa duk kasashen Afirka 54 a wannan lokaci da duniya ke cikin mawuyacin hali.