Kotu ta jaddada hukuncin Zuma
September 17, 2021Talla
Sai dai wannan shari'ar ba ta shafi sakin Zuma da aka yi bisa dalilai na rashin lafiya a farkon wannan watan, batu da ya haifar da cece ku ce kan zargin da ake masa.
Daurin da aka yi masa a watan Yuli ya janyo mafi munin tashe tashen hankulan siyasa da ba a taba ganin irinsa a tarihin kasar tun bayan na lokacin nuna wariyar launin fata na Apartheid, rikicin da ya jagorancin dibar ganima a sassa daban daban na kasar.
Mai shekaru 79 da haihuwar ya nemi kotun tsarin mulkin Afirka ta Kudu da ta soke hukuncin daurin watanni 15 da ak masa saboda, kin bayyana a kotu domin amsa tambayoyi kan zargin cin hanci da karbar rashawa.