Jacob Zuma zai fuskanci shari'a
March 16, 2018Talla
Babban mai gabatar da kara Shaun Abrahams ya bayyana cewar tsohon shugaban ya jima kasar na zarginsa da manyan laifukan cin amana wadanda hukumar shari'ar kasar ta yi watsi da su a baya lamarin da ya ba shi damar shugabancin kasar,ya kuma kara da cewar daga cikin tsoffin laifukan da aka samu Jacob Zuma da su akwai batun cinikin makamai tun a shekara ta 1990 lokacin da ya ke mataimakan shugaban kasar ko da ya ke a halin yanzu ya karyata wadannan zarge-zarge tare da sukar masu gabatar da karar in da ya kira su da wadanda ba su san aikin su ba.