Jacob Zuma zai gurfana a gaban kotu
March 26, 2018Talla
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma zai bayyana a gaban kotu ranar shida ga watan Afrilu don ya fiskanci tuhuma da a ke masa ta wakaci ka tashi da kudi sama da dala miliyan dubu biyu na kudin makamai kamar yadda lauyansa ya bayyana a wannan rana ta Litinin.
Hukumar da ke shigar da kara a Afirka ta Kudu ta bayyana a farkon wannan wata cewa za ta gurfanar da Zuma kan tuhuma goma sha shida a badakalar da ta shafi cin hanci da rashawa da karkatar da kudin al'ummar kasa da sauransu. Wannan dai ana masa wani kallo na ci gaba a nahiyar da ba kasafai a ke gurfanar da shugabanni ba a kotu.