SiyasaKamaru
Jigo na 'yan adawar Kamaru Anicet Ekane ya mutu
December 1, 2025
Talla
Anicet Ekanem ai shekaru 74 ya mutu a Yaoundé, inda aka mayar da shi can bayan an kama shi a ƙarshen watan Oktoba a Douala, wanda har yanzu ba a san ainihin yanayin mutuwarsa ba.
Anicet jigo na jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta 'yan kishin ƙasa, wato Manidem, kuma mai goyon bayan jagoran adawa Issa Tchiroma Bakary. An kama shi a ranar 24 ga Oktoba a Douala, a jajibirin wallafa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a hukumance.