1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jagoran adawa a Chadi ya zama firamnista

January 1, 2024

A kokarin neman sasantawa da masu hamayya a Chadi, gwamnatin kasar ta nada madugun adawa a matsayin sabon firamnista. Ba da jimawa ba ne dai jagoran adawar ya koma gida.

Succès Masra, sabon firaministan Chadi
Succès Masra, sabon firaministan ChadiHoto: Julien Adayé/DW

An nada madugun adawar Chadi Succès Masra a matsayin firaministan gwamnatin rikon kwaryar kasar, kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar.

Ana dai kallon nadin madugun adawa Masra, wanda ya koma kasar bayan wata yarjejeniya da gwamnatin mulkin soji, a matsayin wata hanya ta neman kwantar da hankalin 'yan adawa bayan zaben raba gardamar da suka bijire masa a a ranar 17 ga watan Disamba.

Firaminista Succes Masra, ya tsere daga kasar ne bayan kashe-kashen da sojojin juyin mulki suka yi wa masu zanga-zanga a ranar 20 ga watan Oktoban bara a N'Djamena babban birnin kasar.

Gwamnatin Janar Mahamat Idriss Déby Itno ta kwace iko cikin watan Afrilun baran ce dai ta ba da sammacin kama shi a lokacin da aka yi bore, abin kuma da ya sanya shi tserewa daga Chadin.