1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jagoran adawar Chadi Succes Masra ya nemi soke zaben kasar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 13, 2024

Masra ya tabbatar da cewa suna da hujjoji da na hotuna da fayafayan bidiyo da ke nuna yadda sojoji suka yi awon gaba da akwatunan zabe, sannan suka cusa kuri'u, suka kuma kirga a boye

Hoto: Issouf Sanogo/AFP

Jagoran adawar kasar Chadi da ya zo na biyu a zaben shugaban kasa da ya gabata Succes Masra, ya shigar da korafi gaban kotun tsarin mulkin kasar yana neman ta soke zaben da shugaba Mahamat Idriss Deby ya lashe, bisa zargin almundahana.

Karin bayani:Takun saka kan sakamakon zaben Chadi

Succes Masra wanda ke rike da kujerar firaministan kasar gabanin zaben, ya shigar da korafin nasa ne ranar Lahadi, yana mai cewar jami'an tsaro sun kama tarin mambobin jam'iyyarsa tare da zarginsu da mallakar takardun bogi domin shiga zabe, kamar yadda mataimakinsa a takarar Sitack Yombatina ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.

Karin bayani:Chadi: An zabi Mahamat Idriss Deby

Masra ya tabbatar da cewa suna da hujjoji da na hotuna da fayafayan bidiyo da ke nuna yadda sojoji suka yi awon gaba da akwatunan zabe, sannan suka cusa kuri'u, suka kuma kirga a boye.

Wannan dalili ne ya sanya Mr Masra ke fatan kotun tsarin mulkin kasar za ta yi adalci wajen bankado gaskiyar lamarin.