1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ali Khamenei ya ce mutuwar Sinwar ba ta sanyaya gwiwarsu ba

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 19, 2024

Sanarwar ta Ayatollah Ali Khamenei a Asabar din nan ta ce hakika mutuwar Yahya Sinwar ta girgiza su, to amma ba za su taba yin kasa a gwiwa ba a fafutukarsu da a turance ake kira da Axis of Resistance

Hoto: Iranian Supreme Leader'S Office/ZUMA Press Wire/picture alliance

Jagoran addinin kasar iran Ayatollah Ali Khamenei, ya sanar da cewa kisan da Isra'ila ta yi wa jagoran kungiyar Hamas Yahya Sinwar, ko kadan ba zai sanyaya gwiwar gwagwarmayar da kungiyoyi masu samun goyon bayanta ke yi ba, da ke da muradan yakar manufofin Isra'ila da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, sannan kuma Hamas na nan tsaye daram.

Sanarwar ta Ayatollah Ali Khamenei a Asabar din nan ta ce hakika mutuwar Yahya Sinwar ta girgiza su, to amma ba za su taba yin kasa a gwiwa ba a fafutukarsu da a turance ake kira da Axis of Resistance.

Karin bayani:Isra'ila ta kashe babban kwamandan Hamas na Lebanon

Fafutukar dai ta hada kungiyoyin gwagwarmaya da makamai daga kasashen Iran da Iraqi da Syria, sai Lebanon da Yemen da kuma zirin Gaza.

Karin bayani:Hamas ta harba rokoki zuwa Isra'ila

A wani labarin kuma rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa an harba mata makamai daga Lebanon da jirage marasa matuka, to amma ta samu nasarar kakkabo guda biyu daga cikinsu.

Kuma babu wanda ya samu ko rauni daga harin.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani