1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

Jagoran kasar Bangaladash ya bukaci a kwantar da hankali

August 8, 2024

Shugaban rikon gwamnatin Bangladesh, Muhammad Yunus ya yi kiran da a kwantar hankali a fadin kasar, sakamakon zanga-zangar da ta kawo karshen mulkin tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina a ranar Litinin.

Jagoran gwamnatin Bangladesh, Muhammad Yunus
Sabon jagoran gwamnatin Bangladesh, Muhammad Yunus Hoto: Raphael Lafargue/abaca/picture alliance

Cikin wani sakon da ya aike wa al'umar Bangaladesh din daga birnin Paris na kasar Faransa a ranar Laraba, Muhammad Yunus ya yi kiran matasa masu zanga-zanga da su dakatar da duk wani bore, ganin yanzu lokaci ne da ya shirya domin kama aikin gina kasa.

A yau Alhamis ne ake sa ran zai koma kasar bayan amsa kiran matasa da ya yi na karbar ragamar shugabanci.

Muhammad Yunus mai shekaru 84 da ya taba samun lambar yabo ta Nobel a fannin zaman lafiya, fitaccen mai sukar lamirin gwamnati ne, sannan ya yi kaurin suna wajen hamayyar siyasa da tsohuwar firaminista Sheikh Hasina.

Sheikh Hasina dai ta arce zuwa Indiya ne a ranar Litinin, bayan mataki na murabus da ta dauka.