Jagoran NATO ya bukacin bai wa Ukraine makamai
December 3, 2024A wannan Talata Sakatare Janar na kungiyar tsaron NATO, Mark Rutte ya bukaci kasashe mambobin kungiyar su kara taimakon kasar Ukraine da makaman da take bukata maimakon tattauna yuwuwar kawo karshen yakin da ke faruwa da Rasha. A cewar Rutte kasar ta Ukarine abin da take bukata shi ne makamai masu linzami da na kariya.
Karin Bayani: Ya Koriya ta Arewa za ta sauya yakin Ukraine?
Shi dai Mark Rutte sakataren kungiyar ta NATO ya fadi haka a wajen taron ministocin harkokin wajen kungiyar da ke wakana a birnin Brussels na kasar Beljiyam. Haka na faruwa yayin da Donald Trump ke shirin zama sabon shugaban Amurka, wanda ya yi alkawarin neman hanyar kawo karshen yakin da ke faruwa sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine.
Ana sa bangaren Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce samun tabbacin tsaro daga kasashen Yamma gami da makaman da suka dace ke zama hanyar samun zaman lafiya tsakanin kasarsa da kuma Rasha.