Jagorar adawar Faransa Le Pen na fuskantar tuhuma a kotu
September 30, 2024A Litinin ce 30.09.2024, jagorar 'yan adawar kasar Faransa Marine Le Pen za ta fara gurfana a gaban kotu tare da wasu mukarrabanta, don fuskantar tuhuma kan almundahar kudi da almubazzranci da dukiyar kasa. Daga cikin sauran mutane 28 da ke fuskantar tuhumar, har da mahaifinta Jean-marie Le Pen, wanda shi ne ya kafa babbar jam'iyyar adawar ta National Rally.
Karin bayani:Faransa: Bardella ya maye gurbin Le Pen
Zarge-zargen na da alaka da badakalar da ta wakana daga shekarar 2004 zuwa 2016, inda ake zargin Marine da mahaifinta da karbar Euro miliyan 7 daga hannun majalisar dokokin tarayyar Turai, amma suka karkatar da akalar kudin zuwa ga gina jam'iyyarsu. Da zarar an same su da laifin, za su fuskanci hukuncin daurin shekaru 10 a kurkuku da tara, da kuma haramta musu shiga siyasa har na tsawon shekaru biyar.