Jagorar jam'iyyar AfD ba ta da niyyar shiga zabe
April 19, 2017Talla
Frauke Petry, jagorar jam'iyyar masu adawa da baki ta AfD ta bayyana a ranar Laraban nan cewa ba za ta jagoranci yakin neman zaben jam'iyyar ba a zaben ranar 24 ga watan Satimba.
A jawabin da ta fitar na bidiyo a shafinta na Facebook ta yi jawabi kamar haka:
"A kokari na kawo karshen duk wani cece-ku-ce na yi wannan hoton bidiyo inda na ke cewa babu wani tsari daga bangarena na jagorantar jam'iyyar a matsayin 'yar takara ko shiga a dama da ni a neman wata babbar kujerar shugabanci".
A karshen mako ne dai jam'iyyar za ta yi babban taro inda anan ne za ta zayyana 'yan takara da za su jagoranci jam'iyyar ta AfD a kokari na danganawa majalisar dokokin Jamus a karon farko.