1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagorar 'yan adawar Taiwan ta gana da shugaba Xi Jinping na

April 10, 2026

Shugaba Xi Jinping ya ce jagorar 'yan adawar Taiwan, Cheng Li-wun ta jaddada yakininta kan makoma daya da China da Taiwan suka sa a gaba.

Shugaban China Xi Jinping da jagorar 'yan adawar Taiwan, Cheng Li-wun
Shugaban China Xi Jinping da jagorar 'yan adawar Taiwan, Cheng Li-wun Hoto: Xie Huanchi/Xinhua/IMAGO

A ganawar shugabannin a birnin Beijing, bangarorin biyu sun ce barakar da ake samu da ke haddasa rarrabuwar a tsakanin China da Taiwan na kan hanyar dinkewa. Tuni ziyarar ta janyo cece-kuce a fadin Taiwan inda masu adawa da manufofin Cheng Li-wun ke ganinta da nuna zakewa kan manufifin Bejin fiye da kima.

Karin bayani:Taiwan na bukatar zaman lafiya da China 

Tun a shekarar 2016 ne dai gwamnatin Chinar ta dakatar da duk wata hulda da manyan masu fada ji a siyasar Taiwan bayan da jam'iyyar Democrat ta yankin ta yi fatali da kasancewar Taiwan  a karkashin ikon wani bangare na kasar Sin, inda ta kara karkata alakarta da Amurka, lamarin da ya kai kasar ga gudanar da gagarumin atisayin soji a tekun yankin, a wani mataki na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.