Jagororin da ke rikici da juna a Sudan sun amince da ganawa
December 11, 2023Jagororin bangarori biyu da ke rikici da juna a Sudan sun amince da ganawar keke-da-keke domin tattauna hanyoyin bi na tsagaita wuta, tare da kawo karshen zubar da jinin da aka shafe tsawon watanni ana yi a kasar, kamar yadda kungiyar raya kasashen Gabashi da kuma na Kahon Afirka IGAD ta sanar.
Karin bayani:Hari kan dam na barazanar haddasa ambaliyar ruwa a Sudan
Sanarwar ta fito ne bayan kammala taro a karshen mako a kasar Djibouti, da ya samu halartar Janar Abdel-Fattah al-Burhan da ke jagorantar Sudan, yayin da mai adawa da shi kuma jagoran dakarun RSF Janar Mohammed Hamdan Dagalo da aka fi sani da Hemedti da ba san inda yake ba aka tattauna da shi ta wayar tarho a taron.
Karin bayani:Dubban yara da suka tsere daga Sudan zuwa Chadi na fama da yunwa
Rikicin Sudan din ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu goma, a dalilin gwagwagwar kwatar ikon mulkin kasar tsakanin wadannan manyan Janar guda biyu da ke ikirarin shugabancin kasar, wadda ta fada cikin rikicin shugabanci tun bayan da su biyun suka hada kai wajen hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir.