Jagororin EU sun amince da kara wa von der Leyen wa'adi
June 28, 2024![](https://static.dw.com/image/69374644_800.webp)
Jagororin kungiyar tarayyar Turai EU sun amince da kara wa Ursula von der Leyen wa'adin mulkin shugabancin kungiyar a hukumance, a taron da suka gudanar a Brussels, kamar yadda shugaban majalisar kungiyar Charles Michel ya tabbatar a shafinsa na X.
Karin bayani:Kasashen Turai na shirin zaben shugaban EU
Bisa yarjejeniyar da jagororin suka cimma yayin taron, sun amince da nadin tsohon firaministan Portugal Antonio Costa a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin EU, sai kuma firaministan Estonia Kaja Kallas da zai karbi mukamin babban jami'in diflomasiyyar kungiyar.
Karin bayani:Ursula von der Leyen na da muradin sake neman shugabancin EU
Wani sako da firaministan Poland Donald Tusk ya wallafa a shafinsa na X, ya tabbatar da cewa wadanda aka bai wa sabbin mukaman sun amince su karba.